Shearer ba zai koma Newcastle ba

Alan Shearer
Image caption Shearer ya ce yana jin dadin aikinsa na hasashen wasanni

Tsohon kyaftin din Ingila Alan Shearer ya ce dan karamin lokacin da ya yi kocin Newcastle a shekarar 2009 ya ishe shi, ba zai sake dawowa jan ragamar kungiyar ba.

Shearer ya bar buga wa Newcastle wasa a shekarar 2006, kuma ya bar tarihin dan wasan da ya fi kowo zura kwallo a kungiyar, kafin ya koma aikin hasashen wasannin kwallon kafa.

Shearer ya ce "Rabona da harkar kwallon kafa kimanin tsawon shekaru hudu, kuma ba na fatan sake tsunduma a harkar wasa, jagorantar kungiya a wasanni takwas ba ta hana kungiyar Newcastle faduwa daga gasar Premier ba."

Ya kara da ce wa" Ina matukar jin dadin aikin da nake a yanzu kuma kuma na yi sa 'a da na samu aikin, ko zan sake dawowa harkar koyarwa ? Amsa a'a.