Bassong ya sabunta kwangilarsa a Norwich

Image caption Sebastien Bassong

Kyaftin din Norwich, Sebastien Bassong ya sabunta yarjejeniyarsa don ci gaba da taka leda a kulob din zuwa shekara ta 2016.

Dan wasan mai shekaru 27, ya bar Tottenham a bara don komawa kungiyar Norwich.

Dan kwallon Kamaru din ya ce ya ji dadin wannan sabuwar kwangilar tare da kungiyar.

Bassong ya buga wa Norwich wasanni 47, inda ya ci kwallaye uku tun komawarsa a shekara ta 2012.