QPR za ta gina katafaren filin wasa

Image caption Tsohon filin wasan QPR ba ya cin 'yan kallo da yawa

Kungiyar Queens Park Rangers ta bayyana shirinta na gina katafaren sabon fili a yankin arewa maso yammacin London.

Sabon filin wasan mai cin 'yan kallo 40,000 za a gina ne a unguwar Old Oak, don maye gurbin filin dake titin Loftus a unguwar Shepherds Bush.

Idan aka kamalla gina filin wasan za a sa masa suna New Queens Park.

Shugaban QPR, Tony Fernandes ya ce " Filin dake titin Loftus , wuri ne na musamman ga kungiyarmu da magoya, amma muna bukatar filin dake daukan 'yan kallo fiye da 18,000."

Yanzu haka dai mahukanta kungiyar ta QPR na tattauna da karamar hukumar Hammersmith & Fulham a London kan wannan katafaren filin wasan.

Karin bayani