Bana bakin ciki da Man City - Wenger

Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger, ya ce ba ya bakin ciki da tawagar Manchester City, a daidai lokacin da su ke shirin fafatawa a ranar Asabar a filin Etihad.

Kocin City, Manuel Pellegrini ya kashe fiye da fan miliyan 90 wajen sayen 'yan kwallo biyar a kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Agusta.

Wenger yace "City na da tawaga mai karfi, amma bana kishi dasu."

Pellegrini wanda ya hade da City a watan Yuni, ya sayi Alvaro Negredo a kan fan miliyan 22, da Stevan Jovetic a kan fan miliyan 20, sai Fernandinho a kan fan miliyan 30 da Jesus Navas a kan fan miliyan 14.9 sai kuma Martin Demichelis a kan fan miliyan 4.2.

A yanzu haka dai Arsenal ce kan gaba a teburin gasar Premier inda ta dara Liverpool da maki biyar.

Karin bayani