Man City ta Casa Arsenal daci 6 da 3

Image caption Kwallon da Negredo ya ci Arsenal

Manchester City ta aike da babban sako ga sauran abokan hammaya a Ingila, bayan ta lallasa Arsenal daci shida da uku a gasar Premier.

Yanzu tazarar dake tsakanin City da Arsenal ya koma maki uku.

'Yan wasan da suka ci wa City kwallo sune; Agüero da Negredo da Fernandinho da Silva da kuma Yaya Touré, a yayinda Walcott da Mertesacker suka ci wa Arsenal kwallo.

Sakamakon sauran wasanni:

*Cardiff 1 - 0 West Brom *Chelsea 2 - 1 Crystal Palace *Everton 4 - 1 Fulham *Newcastle 1 - 1 Southampton *West Ham 0 - 0 Sunderland *Hull 0 - 0 Stoke

Karin bayani