BBC za ta karrama Sir Alex Ferguson

Sir Alex Ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson ya kwashe shekaru 26 a United

Sashin wasanni na BBC zai karrama tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson a matsayin fitaccen mutumin da ya ba da gudunmawa a harkar kwallon kafa a shirinta na karo na 60.

Ferguson dan kasar Scotland mai shekaru 71 ya yi ritaya daga kocin United a watan Mayu, bayan da ya share shekaru 26 yana horar da kungiyar.

Kocin ya lashe kofuna 38 da suka hada da kofunan Premier 13 da kofunan zakarun Turai biyu da kofunan kalubale biyar da kuma League cup guda hudu.

Daraktan wasanni ta BBC Barbara Slater ta ce "muna son mu karrama shi da kyautar Diamond Award ganin irin gudunmawar da ya baiwa harkar wasan kwallon kafa da mahimmiyar kyauta.