Fifa:Raja Casablanca ta doke Monterrey

Raja Casablanca
Image caption Raja Casablanca na fatan kaiwa wasan karshe

Kungiyar kwallon kafa ta Raja Casablanca ta Morocca ta kai wasan kusa dana karshe a kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyi, bayan data lashe Monterrey ta Mexico da ci 2-1 a karawar da suka yi a Agadir.

Raja za ta kara da Atletico Mineiro zakaran kofin Copa Libertadores a wasan kusa dana karshe.

Kungiyar Guangzhou zakaran Asia daga China za ta kara da zakaran Nahiyar Turai Bayern Munich, Guangzhou ce ta zare Al Ahly zakaran kofin kungiyoyin Afrika.

Wannan shine karon farko da Nahiyar Afrika ta karbi bakunci gasar kofin zakaraun kungiyoyin nahiyoyi ta duniya da a baya ake kiransa da Intercontinental Cup.