United ta casa Aston Villa 3-0

United Villa
Image caption united ta farfado daga rashin nasarar wasanni biyu a jere da tayi a gida

Manchester United ta doke Aston Villa da ci 3-0 har gida a karawar da suka yi a gasar cin kofin Premier wasan sati na 16.

Danny Welbeck dan wasan United shine ya zura kwallaye biyu a raga, daga baya Tom Cleverley ya kara kwallo ta uku.

Nasarar da kungiyar ta samu ya bata damar samun maki uku rigis, United ta samu maki biyu kacal a wasanni hudu da ta buga a baya, kuma ta kaucewa rashin nasara a wasanni uku a jere a Premier, rabonta da haka tun Disamba 2001.

Har yanzu kungiyar tana da tazarar maki 10 tsakaninta da Arsenal wacce take matsayi na daya a teburi, kuma tazarar maki shida tsakaninta da kungiyoyi hudun farko a teburin Premier.