"Muna karancin zura kwallaye a raga"

Jose Mourinho
Image caption Kocin na matukar son ganin 'yan wasan gaba su dunga zura kwallaye da raga

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce kungiyarsa ba za ta iya lashe kofi ba a bana, saboda fitattun 'yan wasan gabanta basa zura kwallaye a raga.

Chelsea ta doke Crystal Palace da ci 2 da 1, kuma tazararta maki biyu tsakaninta da Arsenal wacce take matsayi na daya a teburi, kafin su kara ranar 23 ga watan Disamba a Emirates.

Mourinhi ya shaidawa BBC ce wa "bana jin muna daga cikin kungiyar da za ta dauki kofi, domin bamu da dan wasan da zai zura kwallaye 30 shi kadai a bana."

Daga cikin kwallaye 32 da Chelsea ta zura a bana, kwallaye biyar ne fitattun 'yan wasanta masu zura kwallo a raga suka zura mata wanda Fernando Torres da Samuel Eto'o suka zura kwallaye biyu sai Demba Ba da ya zura kwallo daya.