UEFA: Litinin za ta fitar da jaddawali

Uefa Draws
Image caption Kociyoyin na fatan haduwa da kungiyoyin da za su iya lashe wa cikin sauki

Kungiyar Arsenal da Chelsea da Manchester City da Manchester United na jiran jaddawalin wasan kungiyoyi 16 da suka rage a kofin zakarun Turai da za a fitar ranar Litinin.

Chelsea da Manchester United na kokarin kauce wa haduwa da manyan kungiyoyi, ganin sun jagoranci rukunansu, kuma suna cikin fitattun kungiyoyi takwas da aka ware.

Arsenal da City ba sa cikin fitattun kungiyoyin domin sun kare a matsayi na biyu a rukuni, za kuma a iya hada su da Bayern Munich ko Barcelona ko Real Madrid, kuma kungiyoyin da suka fito daga kasa daya ba za su hadu da juna ba.

Chelsea za ta iya haduwa da AC Milan ko Bayer Leverkusen ko Galatasaray ko Olympiakos ko Zenit St Petersburg.

Fitattun kungiyoyi da aka ware: Atletico Madrid da Barcelona da Bayern Munich da Borussia Dortmund da Chelsea da Manchester United da Paris St-Germain da Real Madrid

Wadanda ba fitattu ba: AC Milan da Arsenal da Bayer Leverkusen da Galatasaray da Manchester City da Olympiakos da Schalke da Zenit St Petersburg.