Casa mu ya kara mana kaimi — Wenger

Arsene Wenger
Image caption Wenger ya ce Arsenal za ta iya lashe kofin Premier a bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce casa su da Mancity ta yi 6-3 a gasar Premier ba zai kawo musu tsaikon daukar kofi a bana ba.

Arsenal ta baiwa City tazarar maki uku a kan teburi, amma Wenger ba ya hangen kungiyar za ta iya kawo musu cikas a kokarin da suke na lashe kofin Premier ba.

Manchester City ta zura kwallaye 58 a gasar Premier a wasannin gida data buga a jere, kuma ta fara lashe wasa ne tun bayan da suka kara da Birmingham aka tashi wasa babu ci a watan Nuwamba 2010.

Kocin City Manuel Pellegrini ya jinjinawa 'yan wasansa musamman da suka caskara wadanda ake hasashen za su zamo hudun farko idan aka kammala gasar bana da suka hada da Arsenal da Manchester United da Tottenham kuma jumulla suka zura musu kwallaye 16.