West Brom ta kori Steve Clarke

Image caption Steve Clarke

West Bromwich Albion ta kori kocin tawagar 'yan kwallonta Steve Clarke.

An sallame shi a ranar Asabar, bayan tawagarsa ta sha kashi a hannun Cardiff da ci daya mai ban haushi, kuma a yanzu kungiyar na da tazarar maki biyu tsakaninta da kungiyoyin da ke matakin nutse wa daga gasar Premier zuwa Championship.

Albion ta samu nasara a wasanni bakwai cikin karawa 34 a gasar Premier a shekara ta 2013.

Keith Downing zai maye gurbinsa a matsayin kocin riko.

Clarke, ne koci na hudu da aka kora a gasar ta bana, bayan Paolo Di Canio a Sunderland, Ian Holloway a Crystal Palace da kuma Martin Jol a Fulham.

Karin bayani