Al Ahly ta roki Aboutrika kar yayi ritaya

Mohamed Aboutrika
Image caption Dan wasan ya bugawa Masar wasanni sama da guda 100

Al Ahly na lallashin dan wasanta Mohamed Aboutrika kar yayi ritaya daga kwallo a karo na biyu, bayan da dan wasan ya ji rauni a karawar da suka yi a gasar kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.

Dan kwallon ya ji rauni ne a wasan daf da na karshe da suka fafata ranar Asabar da Guangzhou zakarar Asia, kuma suka yi rashin nasara da ci biyu da nema.

Guangzhou za ta fafata da Bayern Munich a wasan daf da na karshe.

Kocin Al Ahly Mohamed Youssef ya ce kungiyar tana tattauna wa da dan wasan don ganin ta shawo kansa, kuma bai kamata yayi ritaya a cikin radadin rauni ba, ya kamata yayi ritaya a wasan da baza a manta da shi ba.

Dan wasan ya lashe kofin zakarun nahiyar Afrika da Al Ahly har karo biyar.