CAF: Jaddawalin kofin zakarun Afrika

Caf Championleague
Image caption Hukumar Caf ta raba jaddawalin fara gasar kofin zakaru a badi

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta raba jaddawalin fara gasar cin kofin zakarun Afrika karo na 18 a birnin Marrakech da ke Morocco.

Kungiyoyi 52 ne za su fafata a wasan share fage, kafin a tankade kungiyoyin da za su hadu da Al Ahly ta Masar mai rike da kofin da Coton Sport ta Kamaru da TP Mazembe ta Jamhuriyar Congo da Hilal ta Sudan da CS Sfaxien Tunisia da Esperance Sportive ta Tunisia.

Cikin wasannin da za a fafata sun hada da karawa tsakanin Enyimba ta Najeriya da Ange de Notse ta Togo, Asante Kotoko ta Ghana da Barrack Young Controllers ta Liberia, Raja Casablanca ta Morocco da Diamond Stars ta Saliyo, AC Leopards ta Congo da Rayon Sport ta Rwanda.

Kaizer Chiefs ta Afrika ta kudu zata karbi bakunci Black Africa ta Namibia sai AS V Club ta Jamhuriyar Congo da Kano Pillars ta Najeriya, Al Merreikh ta Sudan da Kampala City Council ta Uganda da kuma karawa tsakanin Zamalek ta Masar da AS Douanes ta Niger.

Za su fara karawa a wasannin farko ranar 7 izuwa 9 ga watan Fabrairun badi, sannan wasa na biyu sati guda baya.

Shima kofin Confederation an fidda jaddawalin wasannin karo na 11 da kungiyoyi 42 za su kafsa a wasan share fage kafin su hadu da kungiyoyin ASEC Mimosas ta Cote d'Ivoire, Ismaily ta Masar, Wadi Degla ta Masar, Djoliba ta Mali, MAS ta Morocco, Bayelsa United ta Najeriya, Warri Wolves ta Nijeriya, El Ahly Shandy ta Sudan, Etoile du Sahel ta Tunisia, Club Athletic Bizertin ta Tunisia da Zesco United ta Zambia.