Cristiano Ronaldo ya bude gidan tarihi

Image caption Cristiano Ronald ya ce zai ajiye dukkanin kyautar da ya samu a gidan tarihi

Dan wasan gaba na Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya bude gidan tarihi inda zai rika ajiye kofunan da suka ci a gasa daba-daban.

Ronaldo, mai shekaru 28 a duniya, yana cikin 'yan wasa uku da Fifa ta ware sunayensu domin yiwuwar lashe gasar zakaran kwallon kafa na duniya a karo na biyu.

Ronaldo ya ce, "Wannan muhimmiyar rana ce a gare ni. Ina so na ci gaba da lashe kyaututtuka don haka idan na lashe gasar zakaran kwallon kafa akwai dakin da na ware domin ajiye ta''.

Ya bude gidan tarihin ne a mahaifarsa ta Madeira inda a halin yanzu aka ajiye fiye da kyautuka125.

Karin bayani