Ba zan yi murabus daga Tottenham ba —Villas-Boas

Image caption Andre Villas-Boas ya ce ba shi ke da alhakin korar kansa ba

Kocin Tottenham, Andre Villas-Boas, ya ce ya dauki alhakin dokewar da Liverpool suka yi musu da ci 5-0 a gida, amma ya ce ba zai yi murabus daga kungiyar ba.

Da aka tambaye shi kan makomarsa a kungiyar, Villas-Boas ya ce: "Ba ni ne zan yanke shawara kan makomata ba.Ba zan ajiye aikina ba domin ni ba mai ajiye aiki ba ne. Abin da kawai nake yi shi ne aiki tukuru tare da 'yan wasa domin samun sakamakon da muke so."

Fafatawar dai ita ce dokewa mafi muni da aka yi wa kungiyar a gida cikin shekaru 16.

Sau daya kawai Tottenham ta yi nasara a wasan da ta buga a gida na Gasar Premier, kuma Manchester City ta doke ta 6-0 a watan jiya.

Karin bayani