UEFA: Manchester City da Barcelona

uefa draw
Image caption A raba jaddawalin kungiyoyi 16 da za su fara karawa a badi

Manchester City za ta kara da Barcelona a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar cin kofin zakarun Turai.

Arsenal ita kuwa za ta karbi bakuncin mai rike da kofin bara Bayern Munich, sai Chelsea data lashe kofin a shekara ta 2012 za ta fafata da Galatasaray, yayinda Manchester United za ta barje gumi tare da Olynpiakos.

Sauran wasannin da za a raba reni sun hada da AC Milan da Athletico Madrid, Bayer Leverkusen da Paris St-Germain, Schalke da Real Madrid da karawa tsakanin Zenit St Petersburg da Borussia Dortmund.

Chelsea da Manchester United za su fara wasannin su a waje, a inda Arsenal da Manchester City za su fara karbar bakunci wasannin su.

Wasannin da za a kara gida da waje za a fara gumurzu a wasannin farko ranar 18 da19 da kuma 25 da 26 ga watan Fabrairu, sai fafatawa ta biyu ranar 11 da 12 da kuma 18 da 19 da watan Maris a badi.