Fletcher na son ganin United a gaba

Darren Fletcher
Image caption Dan kwallon na fatan United ta lashe kofuna a bana

Dan kwallon Manchester United Darren Fletcher ya ce ya na fatan zai taimakawa kungiyar komawa ganiyarta, bayan da ya dawo daga doguwar jinyar rashin lafiya.

Dan kwallon mai shekaru 29 ya yi fama da ciwon toshewar hanji a tsawon shekaru uku, kafin yayi jinyar shekara guda ya kuma dawo wasa da kungiyar a karawar da suka lashe Aston Villa da ci 3-0 ranar Lahadi.

United na fama da rashin tabuka rawar gani a gasar Premier bana tun lokacin da sabon koci David Moyes ya koma kungiyar, sai dai lashe Villa da kungiyar ta yi yasa ta koma matsayi na takwas a teburi da tazarar maki 10 tsakaninta da Arsenal wacce take matsayi na daya.

Fletcher ya ce"ya kamata mu dawo lashe wasanni domin maida kungiyar matsayin da jama'a za su san har yanzu muna nan."