Fifa ta dakatar da Simunic na Croatia

josip simunic
Image caption josip simunic

Dan wasan bayan Croatia Josip Simunic ba zai shiga gasar cin kofin duniya ba bayan da Fifa ta dakatar da shi tsawon wasanni 10 saboda nuna wariya.

Simunic na kungiyar Dinamo Zagreb ya jagoranci magoya bayan Croatia ne wurin rera wakar dake da dangantaka da goyon bayan 'yan Nazi bayan da kasarsa ta samu nasara 2-0 a karonsu da Iceland.

Haka kuma Fifa ta ci tarar Simunic £20,000 duk da ya ce babu wata manufa ta siyasa a wakar da ya yi.

Dakatar da Simunic za ta fara aiki ne daga wasan farko na gasar cin kofin duniya ta 2014 inda Croatia za ta kara da mai masaukin baki Brazil a Sao Paulo.

Simunic na daga cikin 'yan wasan da Croatia ke ji da su kuma ya buga mata wasannin cin kofin duniya biyu da na cin kofin Turai uku.