Ana zargin Gattuso da sayar da wasa

Gennaro Gattuso
Image caption Gennaro Gattuso

Ana binciken fitaccen dan kwallon Italia, Gennaro Gattuso game da zargin sayar da wasa.

'Yan sanda sun kuma zargi wasu mutanen hudu da laifin sayar da wasanni a rukunin kwallon kafa na Serie A shekaru uku da suka wuce, abinda ya sa adadin wadanda aka kama game da badakalar ya zarta 50.

Gattuso ya shahara wurin bugawa Italia wasa ne da kuma kungiyar AC Milan tsawon shekaru 10 da suka wuce.

Ya dago kofin kwallon kafa na duniya a 2006 sannan kuma ya dau kofin Turai sau biyu.

Bara Gattuso ya yi ritaya daga wasa ya kuma zama kocin kungiyar Sion ta Switzerland.