Glenn Hoddle na son komawa Spurs

Glenn Hoddle
Image caption Glenn Hoddle

Tsohon kocin Tottenham Hotspurs, Glenn Hoddle na fatan sake komawa kungiyar a karo na biyu.

Hoddle, wanda tsohon kocin Ingila ne, ya horar da kungiyar ne tsakanin shekarun 2001 da 2003 kuma ya na cikin wadanda aka ambata a matsayin magadan Andre Villas-Boas da aka kora ranar Litinin.

Sauran wadanda aka ambata sun hada da tsohon kocin Ingila Fabio Capello, kocin Swansea Michael Laudrup da kuma daraktan Tottenham Franco Baldini.

An sallami Villas-Boas bayan watanni 17 a White Hart Lane ne bayan da kungiyar ta sha kaye 5-0 a hannun Liverpool, abin da ya mai da ita ta bakwai a rukunin Premier.

Yanzu haka dai kungiyar ta nada Tim Sherwood a matsayin kocin rikon kwarya.