Suarez ne gwarzon 'yan kallo a bana

Luis Suarez
Image caption Dan wasan ya ce a bana ya taka rawar gani sosai

Dan wasan Liverpool Luis Suarez ya lashe kyautar gwarzon dan wasa da 'yan kallo su ka zaba a bana.

Suarez a lokacin da yake karbar kyautar ya ce "abin girmama wa ne a wajena dana karbi kyauta daga magoya bayan kungiyoyi."

Ya kara da ce wa kyautar ba tashi ba ce shi kadai har da 'yan wasan Liverpool da kociyoyi da magoya bayan kungiyar.

Dan wasan ya ce bana ta yi masa halarci," kuma kowa ya san yadda nake son buga kwallo a koda yaushe, na kuma yi murna matuka ganin ni da kungiyata muna kokari a bana. Kuma za mu tunkari badi da fatan samun nasarori."

Daga karshe ya yi fatan badi zai kara kwazo tare da kungiyarsa Liverpool da kasarsa Uruguay da nufin samun nasarori.