Mourinho ya koka da rashin zura kwallaye

Jose Mourinho
Image caption Muna karancin zura kwallaye a raga a bana

Kocin Chelsea ya ce ya damu matuka da kungiyar sa bata zura kwallaye matuka, kuma dalilin da yasa Sunderland ta zare su daga Capital One Cup.

Chelsea duk da ita tafi taka rawa a karawar da suka yi a jiya a wasan daf da na kusa da karshe, amma ta yi rashin nasara da ci 2-1.

Mourinho ya ce "mun buga kwallon da ta kayatar matuka, kuma munyi rashin nasara ne sakamakon 'yan wasan gaban mu basuyi amfani da damar da suka samu ba.

Chelsea ce ta fara zura kwallo a lokacin da Lee Cattermole ya ci kansu da kansa, kafin daga baya Fabio Borini ya farke kwallo aka tafi karin lokaci bayan an tashi wasa 1-1.