Sunderland ta doke Chelsea 2-1 a Capital One

Gus Poyet
Image caption Kocin Sunderland, Gus Poyet

Sunderland ta kai matakin daf da na karshe a gasar cin kofin Capital One bayan da ta yi nasara kan Chelsea a karin lokaci.

Chelsea ce tafi taka rawa a wasan sai dai ko kwallo dayan ma da ta samu, dan wasan Sunderland Lee Cattermole ne ya ci gida.

Hakan ya sa Chelsea ta dau hanyar samun nasara amma kwallon da Fabio Borini ya farke ta sa aka kai ga karin lokaci.

A karin lokacin ne Sunderland ta mamaye wasan inda Ki Sung-Yueng ya jefa kwallon da ta basu nasara.