Naki buga gasar Premier inji Traore

Ibrahima Traore
Image caption Gasar Premier tayi fice a duniya kowa ita yake hange

Dan kwallon Guinea mai buga wasa a Stuttgart Ibrahima Traore ya sanar da cewar ya sami goron gayyata daga kungiyoyin Premier a kakar bana, amma yaki amincewa.

Dan kwallon mai shekaru 25 ya kwashe shekaru bakwai yana buga kwallo a Jamus, ya kuma koma kungiyar Stuttgart a watan Mayun 2011.

Traore ya sheda wa BBC cewa "na samu gayyata gada kungiyoyin Premier sau da dama, gasar Premier itace tayi fice a duniya babu tantama, kuma kowa yana son buga gasar, amma ina jin dadin wasa a Stuttgart."

Dan wasan ya bugawa Stuttgart wasanni 50 a gasar Bundesliga ya kuma jefa kwallaye 6 a raga.