UEFA ta hukunta Olympiakos da Zenit

Uefa Olympiakos
Image caption Ana fargabar kunna hayaki mai tartsatsi zai iya jawo hasarar rayuka

Olympiakos za ta karbi bakuncin Manchester United wasan farko a gasar kofin zakarun turai a wasan 'yan kungiyoyi 16, tare da rufe wasu sashin filin wasan kungiyar.

Uefa ta umarci rufe wasu sashin filin wasan ne sakamakon kalamun wariya da kunna hayaki mai tartsatsi a karawar da suka yi da Anderlecht ranar 10 ga watan Disamba a wasan cikin rukuni na gasar.

Haka kuma anci tarar kungiyar Yuro 30,000, sai dai kungiyar ta roki hukumar na ta janye tarar.

Manchester United za ta ziyarci Girka a karawar da za su yi ranar 25 ga watan Fabrairun badi.

Itama kungiyar Zenit St Petersburg za ta kara da Borussia Dortmund tare da rufe wasu sashin filin wasanta.

An hukunta Zenit dake Rasha bisa samun magoya bayan kungiyar da kalamun wariya da kuma kunna hayaki mai tartsatsi da kawo tarnakin wasa da 'yan kallon kungiyar suka yi a wasan da Austria Vienna ta casa ta da ci 4-1.