Wilshare ya amince da tuhumar FA

jack wilshere
Image caption Dan wasan zai yi hutun wasanni biyu idan an same shi da laifi

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshare ya amince da tuhumar da hukumar kwallo ta yi masa na cin zarafi 'yan kallo da nunin yatsa, sai dai bai yarda da hukuncin hutun wasanni biyu ba.

Dan wasan mai shekaru 21, an dauki hotonsa a Talabijin lokacin da yaci zarafin magoya bayan Mancester City a wasan da aka caskara su da ci 6-3 a Ettihad.

Koda yake alkalan wasa ba suga lokacin da dan wasan ya ci zarafin ba, amma an dauki lokacin da ya daga yatsansa ga 'yan kallo a bidiyo, kuma tsoffin alkalai suka zauna suka kalla sannan suka tuhumce shi.

Za a zauna sauraren karar ranar Alhamis.

Idan hukuncin da aka yanke ya tabbata, dan wasan ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Chelsea ba a Emirates ranar 23 ga watan Disamba da karawa da West Ham ranar 26 ga watan Disamba a gasar Premier.