Iniesta ya sabunta kwantaragin shekaru 3

Andres Iniesta
Image caption Dan wasan zai ci gaba da bugawa Barcelona kwallo

Dan wasan Barcelona Andres Iniesta zai ci gaba da bugawa kungiyar wasa bayan da ya sabunta kwantaraginsa na tsawon shekaru uku.

Tun farko kwantiraginsa da kungiyar za ta kare a watanni 18 masu zuwa, sai dai kungiyar ta sha fadar cewa a shirye take ta tsawaita zaman dan wasan dan kasar Spain a cikinta.

Shugaban kungiyar, Sandro Rosell, shi ne ya sanar da cimma jarjejeniyar, yana mai cewa dan wasan yana da sauran shekaru da zai ci gaba da buga wa kungiyar kwallo.

Rosell ya ce, "dan wasan zai ci gaba da buga mana kwallo har zuwa shekarar 2018, daga nan za mu ci gaba da sabunta kwantiragi da shi a kowacce shekara iya tsawon kokarinsa a wasanni''.

Iniesta ya bugawa Barcelona wasanni 479 tun daga lokacin da aka dauko shi daga Albacete a shekarar 1996 sannan yana da shekaru 19, ya kuma lashe kofunan zakarun turai guda uku da na La Liga guda biyu.