An raba City da United a Capital One

Image caption David Moyes na United da Manuel Pellegrini na City.

Manchester United da Manchester City ba za su hadu da juna ba a wasan kusa da na karshe na cin kofin Capital One.

United, wacce ta casa Stoke 2-0 za ta kara da Sunderland ne wacce ta bai wa Chelsea mamaki sanadiyyar kwallon Ki Sung-Yueng a karin lokaci.

A daya karawar kuma, City - wacce ta lallasa Leicester - za ta buga da West Ham, wacce ta farke, ta kara, ta samu nasarar 2-1 a kan Tottenham.

Kungiyoyin za su fafata a zagayen farko ne a makon shida ga Janairu yayinda zagaye na biyu zai biyo bayan makonni biyu.

Ba sake

A zagayen farko City da Sunderland ne za su buga wasanninsu a gida.

Wannan jadawalin na nufin ba za'a maimaita wasan kusa da na karshe na 2009-10 ba, inda kwallon da Wayne Rooney ya saka da ka ta kwato United daga kayen da ta sha a zagayen farko a hannun City, abinda ya ba ta damar isa wasan karshe.

Idan kungiyoyin biyu na Manchester su ka kai wasan karshe da za'a buga a Wembley, wannan ce damar Moyes da Manuel Pellegrini ta farko ta samawa sababbin kungiyoyinsu wani babban kofi.