Afrika ta kudu za ta kara da Brazil

South Africa Brazil Friendly
Image caption Wasan zai zama gwaji tsakanin Afirka ta kudu da Brazil

Afirka ta kudu ta ce za ta kara a wasan sada zumunci da mai rike da kofin duniya a karo biyar, Brazil ranar 5 ga watan Maris na badi a Johannesburg.

Karawar na cikin shirye-shiryen da Brazil ke yi na karbar bakuncin kofin duniya a badi.

Kungiyar Bafana Bafana na fatan taka rawar gani a wasan, kamar yadda ta doke Spain, mai rike da kofin duniya a wasan sada zumunci da suka kara da ci daya mai ban haushi a watan Nuwamba.

Shugaban kwallon Afrika ta kudu, Danny Jordan, ya ce "taka rawar gani a karawar da za mu yi da Brazil zai kawar da shakkun cewa kasar ta dawo ganiyar wasanninta."

Wannan shi ne wasan sada zumunci na karshe da Brazil za ta buga kafin kofin duniya, kuma za ta yi amfani da zakakuran 'yan wasanta da take sa ran za su wakilce ta a gasar.