A bani kocin Tottenham, in ji Sherwood

Tim Sherwood
Image caption kocin na hangen zai iya kai kungiyar gaci

Mai rikon kwaryar kocin Tottenham, Tim Sherwood, ya ce ya kamata a ba shi kocin kungiyar.

Sherwood, wanda ya karbi kocin kungiyar rikon kwaryar bayan da aka kori Andre Villas-Boas, ya jagoranci kungiyar a wasan da West Ham ta doke su da ci 2-1 a gasar League Cup a wasan daf da na karshe.

Kocin, tsohon dan wasan kungiyar mai shekaru 44, ya ce ya kamata a ba shi ragamar kungiyar ko da yake ba shi ne zai yanke hukuncin hakan ba.

Tsohon dan kwallon Ingila, ya bugawa Tottenham wasa daga 1999 zuwa 2003, ya kuma ce a shirye yake ya jagoranci kungiyar domin zai iya.

Ya shiga tawagar kociyoyin kungiyar a shekarar 2008 a karkashin Harry Redknapp a matsayin jami'in tsare-tsare, kafin shugaban kungiyar Daniel Levy ya ba shi kocin rikon kwarya bayan an sallami Villas-Boas.