"Casa Tottenham zai kara mana kaimi"

Sam Allardyce
Image caption Kocin yana son 'yan wasansa su kara kwazo

Kocin West Ham Sam Allardyce ya ce yana fatan yan wasansa za su kara kaimi a gasar Premier, ganin yadda suka doke Tottenham a kofin Capital One Cup a wasan daf da na kusa da karshe.

West Ham da take matsayi na 17 a teburin Premier, ta doke Spurs wacce ta kori kocinta Andre Villas-Boas's da ci 2-1 har gida, ta samu kaiwa wasan kusa dana karshe.

Wannan itace nasarar farko a cikin wasanni hudu da kungiyar ta kara, Allardyce ya ce"zai dan sarara a yanzu, kuma yana fatan nasarar ta sa 'yan wasansa su kara kwazo a gasar Premier."

West Ham za ta kara da Manchester City a wasan daf dana karshe ranar 6 ga watan Janairun badi.