West Ham ta yi nasarar 2-1 kan Spurs

Modibo Maiga
Image caption Modibo Maiga ne ya zura kwallon da ta ba da nasara.

Kwallaye biyu a minti 10 na karshe ne su ka bai wa West Ham nasara kan Tottenham tare da samun gurbin karawa da Manchester City a wasan kusa da na karshe na gasar kofin Capital One.

Tottenham ne su ka fara ja gaba lokacin da Emmanuel Adebayor ya ci kwallonsa ta biyu tun cikin watan Mayu.

Matt Jarvis ne ya farkewa Hammers kafin Modibo Maiga ya zura kwallon da ta bada nasara saura minti biyar a tashi wasa.

Wannan ne karo na biyu cikin wannan mako da Spurs suka sha kaye a gida bayan da Liverpool ta ragargaje su 5-0, abinda ya haddasa korar kocin kungiyar Andre-Villas Boas.