Kamaru za ta kece raini da Jamus

Image caption Tawagar Indomitable Lions ta Kamaru

Kamaru da Jamus za su buga wasan sada zumunci a Monchengladbach a ranar daya ga watan Yuni kafin a soma gasar cin kofin duniya a Brazil a shekara ta 2014.

Kocin Kamaru, Volker Finke ya nuna dadin fuskantar kasar sa ta haihuwa.

Jamus na rukuni daya ne da kasashen Ghana da Amurka da kuma Portugal.

Ita kuma Kamaru za ta hadu ne da kasashen Brazil da Croatia da Mexico a gasar kofin duniya.

Karin bayani