Cardiff City za ta kori Mackay

Image caption Malky Mackay

Mamallakin Cardiff City Vincent Tan ya umarci kocin kungiyar Malky Mackay da ya ajiye aikinsa ko kuma ya kore shi.

A ranar Litinin ne Tan ya aikewa Mackay sakon i-mel inda ya soki yadda yake tafiyar da kungiyar.

Tan ya soki Mackay game da yadda ya ke daukar 'yan wasa, da yadda yake horar da su da kuma irin sakamakon da suke samu a filin kwallo.

Dan kasuwar na Malaysia ya kuma bayyana kokwanto kan kwarewar tsohon kocin na Watford kan aikinsa.

A baya dai Mackay ya ce ba zai ajiye aikinsa ba.