Suarez ya sabunta kwangilarsa a Liverpool

Image caption Luis Suarez

Luis Suarez ya sanya hannu a sabuwar kwangila tare da Liverpool don ci gaba taka leda a Anfield.

Dan kwallon mai shekaru 26 ya hade ne da Reds a watan Junairun 2011 kuma a kakar wasa ta bana ya zura kwallaye 17 cikin wasanni 11.

Suarez a bisa wannan yarjejeniyar, zai dunga karbar fan dubu 160 a kowanne mako har zuwa karshe kakar wasa ta bana sannan kuma a kakar wasa mai zuwa zai dinga karbar fan dubu 200 a kowanne mako.

Yace "Na ji dadin kulla wannan sabuwar yarjejeniyar tare da Liverpool."

Karin bayani