Liverpool ta hau sama a gasar Premier

Image caption Lius Suarez ya ci kwallaye 19 a kakar wasa ta bana

Luis Suarez ya taimaka wa Liverpool ta hau saman teburin gasar Premier ta Ingila, bayan ya ci kwallaye biyu a wasan da suka doke Cardiff City.

An tashi wasan dai a Anfield, Liverpool na da ci uku Cardiff na da ci daya.

Dan kwallon Uruguay din ya ci kwallon farko a minti na 22 kafin Raheem Streling ya ci ta biyu sai kuma Suarez din ya ci ta uku a yayin da Jordan Mutch ya farke wa Cardiff kwallo daya.

Rawar ganin da Luis Suarez ya taka a wannan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da ya sabunta kwangilarsa a Liverpool inda zai dinga karbar fan dubu 200 a kowanne mako.

Kawo yanzu dai Suarez ya ci kwallaye 19 a gasar Premier.

Karin bayani