United ta doke West Ham da ci 3 da 1

Image caption Young ne ya ci kwallo daya

Manchester United ta doke West Ham da ci uku da daya a wasan da suka buga na gasar Premier a filin Old Trafford.

Danny Welbeck da Adnan Januzaj da kuma Ashley Young ne su ka ci wa United kwallayenta a yayin da Carlton Cole ya farke wa West Ham kwallo daya.

Sakamakon wasannin gasar Premier: *Liverpool 3 - 1 Cardiff *Crystal Palace 0 - 3 Newcastle *Fulham 2 - 4 Man City *Man Utd 3 - 1 West Ham *Stoke 2 - 1 Aston Villa *Sunderland 0 - 0 Norwich *West Brom 1 - 1 Hull

Karin bayani