Ba zan yi ritaya ba inji Mackay

Malky Mackay
Image caption Kocin ya ce ba zai yi ritaya daga aikin sa ba

Kocin Cardiff Malky Mackay ya kara jaddada cewar ba zai yi ritaya daga horar da kungiyar ba, bayan da Liverpool ta casa su a ranar Asabar.

Mai kungiyar Cardiff Vincent Tan, dan Malaysia ya kalli karawar da suka yi rashin nasara da ci 3-1 a filin Anfield, a inda ya sanar da kocin ko ya yi ritaya ko ya kore shi daga aiki.

Mackay, mai shekaru 41, ya ki bayyana makomarsa bayan rashin nasara da suka yi a hannun Liverpool, sai dai ya ce tabbas ba zai yi ritaya daga kocin kungiyar ba.

Ya kuma kara da cewa ba ya jimamin hukuncin da mai kungiyar zai dauka a kansa, bayan da suka tattauna kafin karawarsu da Liverpool.

Shugaban kungiyar Tan, tun da farko ya umarci ciyaman din kungiyar Mehmet Dalman ya fara shirye-shiryen neman wanda zai gaji Mackay kafin ya yanke shawarar korar kocin.