Tottenham ta doke Southampton 3-2

southampton tottenham
Image caption Sherwood na son a bashi kocin Tottenham

Tottenham ta lashe Southampton har gida a gasar Premier wasan sati na 17, da ci 3-2 kuma Adebayor ne ya zura kwallaye biyu daga ciki.

Dan wasan Tottenham Emmanuel Adebayor shi ne ya zura kwallaye biyu, kuma kwallayen farko da ya fara zurawa a kakar Premier bana.

Tottenham karkashin jagorancin kocin rikon kwarya Tim Sherwood, bayan da aka kori Andre Villas-Boas, an fara zura mata kwallo ta hannun dan wasan Southampton Adam Lallana.

Nan take Adebayor ya farke kwallo, sai kwallon Jos Hooiveld da ya ci kansu da kansa, kafin Rickie Lambert ya farke kwallo wasa ya koma 2-2, a inda Adebayor ya kara kwallo ta biyu kuma ta uku da kungiyar ta zura.

Casa Southampton, wacce ta dare matsayi na uku a teburin Premier a watan Nuwamba, yanzu ta kasa lashe wasanni shida a jere, kuma rashin tabuka rawar gani mafi muni tun lokacin da Mauricio Pochettino ya za ma kocin kungiyar a watan Janairu.