Everton ta doke Swansea da ci 2-1

Ross Barkley
Image caption Everton na daga cikin kungiyoyin hudun farko a teburi

Kungiyar Everton ta lashe Swansea har gida da ci 2-1 a gasar kofin Premier wasan sati na 17.

Dan wasan Everton ne Ross Barkley ya zura kwallo ta biyu daga dukan free kick, nasarar da ya kai kungiyar cikin 'yan hudun farko a teburin Premier.

Barkley mai shekaru 20, ya samu damar maki da dama bayan an dawo daga hutu, har da kwallon da ya buga ta doki turke kafin daga baya ya zura kwallo ta biyu.

Da yake kwallayen a wasan zagaye na biyu a ka zura su, Seamus Coleman ne ya fara zura kwallo tun daga yadi na 25, kafin daga baya Dwight Tiendalli ya buga kwallo ta taba mai tsaron bayan Everton Bryan Oviedo ta kuma shiga raga.

Everton ta buga wasanni 10 ba a doke ta ba, kuma tana matsayi na hudu da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool da ke matsayin na daya a tebur.