Mai Cardiff ya fasa korar koci Mackay

Tan Malky
Image caption Kocin zai ci gaba da jagorantar kungiyar a kakar bana

Mai kungiyar Cardiff City Vincent Tan ya janye ikirarin da yayi na zai kori koci Malky Mackay, harma an shirya ranar da za su gana domin dinke barakar da ke tsakanin su.

Tun a ranar Litinin ne Tan ya turawa Mackay sako ta yanar gizo cewa ya ajiye aikinsa ko kuma a kore shi.

Ciyaman din kungiyar Mehmet Dalman ya ce a yanzu komai ya lafa, mai kungiyar ya janye maganar korar kocin, saboda haka zai ci gaba da aiki.

Ya kuma roki magoya bayan kungiyar kar su ta da kayar-baya ga shugaban kungiyar Tan ranar Alhamis lokacin da za su kara da Southampton a gasar Premier wasan sati na 18 a gida.