Ba na gaba da Mourinho in ji Wenger

Wenger Mourinho
Image caption Wenger ya ce lashe wasanni da Arsenal ne a gabansa

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce babu gaba tsakaninsa da kocin Chelsea Jose Mourinho.

A cikin karawa tara da suka yi a tsakaninsu, Wenger bai samu nasara ba a kan Mourinho, sun hadu a baya-bayan nan a gasar kofin Capital One a inda Chelsea ta cire Arsenal a gasar da ci 2-0 a watan Oktoba.

Idan Arsenal ta samu nasara a karawar da za su yi ranar Litinin, za ta koma matsayinta na daya a teburin Premier, matsayin da Liverpool ta dare a yanzu.

Wenger ya ce "babu gaba tsakani na da Mourinho, mun fafata a manyan wasanni sau da dama, amma abin da na sa a gabana shi ne kungiya ta Arsenal da 'yan wasana da taka rawar gani a gasar bana."

Ya kara da ce wa "karawa da za mu yi ranar Litinin da Chelsea ko da ma wace kungiya ce duk daya ne, saboda mafi mahimmaci a tare damu mu koma lashe wasanninmu."

Tsakanin Wenger da Mourinho sun kara a wasanni daban daban har karo tara, Mourinho ya lashe wasanni biyar, suka buga canjaras a wasanni hudu.