Everton ta hau sama a Premier

Image caption Ross Barkley

Kwallon da Ross Barkley ya zura a karshen wasansu da Swansea ta bai wa Everton damar kai wa mataki na hudu a rukunin gasar Premier.

An dai kare rabin lokacin farko ne ba kwallo ko daya.

A rabin lokaci na biyu, Seamus Coleman ya fara tura Everton gaba kafin Bryan Oviedo na Swansea ya farke.

Everton ta buga wasanni 10 ke nan ba tare da faduwa ba, kuma tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool da ke jagorantar rukunin Premier.