A bani koci ko in yi gaba - Sherwood

Image caption Tim Sherwood

Kocin rikon kwarya na Tottenham Tim Sherwood ya ce wajibi ne kungiyar ta bayyana sabon kocinta cikin gaggawa bayan da kafafen yada labaran Netherlands su ka ce da alamu Louis van Gaal ne zai karbi kungiyar bayan kammala gasar cin kofin duniya.

Sherwood, wanda ke neman a nada shi kocin din-din-din, ya jagoranci Spurs ta samu nasarar 3-2 a Southampton ranar Lahadi.

Van Gaal ya ce ya na son komawa rukunin Premier amma sai bayan ya kai Netherlands gasar cin kofin duniya.

Sai dai Tim Sherwood ya ce: "Ba na son aikin nan na minti 10. Ina son a dauke ni koci ko kuma a sallame ni."