Michu zai jinyar makwanni shida

Image caption Michu ya haskaka sosai a kakar wasan da ta wuce

Dan kwallon Swansea, Michu zai yi jinyar makwanni shida saboda tiyatar da aka yi masa a idon sawunsa.

Dan kasar Spain din mai shekaru 27, bai buga wasansu da Everton ba, da suka sha kashi daci biyu da daya.

Kocin Swansea, Micheal Laudrup ya ce " Labarin baida dadin ji."

Michu ya zura kwallaye 28 tun da ya hade da Swansea daga Rayo Vallecano a shekara ta 2012.

Karin bayani