Bafana Bafana ta yi rashin 'yan wasa

Bafana Bafana
Image caption Bafana Bafana

Kungiyar Kaizer Chiefs ta ce ba za ta kyale 'yan wasanta su buga wa Afrika ta Kudu kwallo a gasar cin kofin kasashen Afrika ta masu wasa a gida, wacce kasar za ta karbi bakunci.

Kocin Bafana Bafana Gordon Igesund ya ambato 'yan wasan Kaizer Chiefs guda shida a jerin wadanda za su wakilci kasar a gasar da za'a fafata daga 11 ga Janairu zuwa 1 ga Fabrairu.

Kocin Kaizer Chiefs Bobby Motaung ya ce su na da muhimmin wasa da kungiyar Mamelodi Sundowns ranar 23 ga Janairu sannan kuma su na shirin shiga gasar zakarun nahiyar Afrika.

Wannan na nufin Bafana Bafana ba za ta samu 'yan wasa irin su Itumeleng Khune, Tefo Mashamaite, Tsepo Masilela, Reneilwe Letsholonyane, Siphiwe Tshabalala da Bernard Parker ba.

Afrika ta Kudu dai na cikin rukuni guda da Nigeria, Mali da Mozambique.