An bude kakar wasanni ta Masar

Image caption Rikicin magoya bayan kwallo kan yi tsanani a Masar.

An fara buga wasannin rukunin kwallon kafa na Masar a makare, tare da fatan za'a kammala kakar bana bayan da dalilan tsaro suka hana karasa biyun da suka gabata.

A cikin kakar wasannin ta 2013-14 har da kungiyar Al Masry wacce rikicin da ya barke a wasanta da Al Ahly a garin Port Said a Fabrairun bara ya hallaka fiye da mutane 70.

Rikicin ya tada hankalin kasar tare da jawo dakatar da kakar wasanni ta 2011-12.

Bayan tsaikon kusan shekara guda, aka shiga sabuwar kakar wasanni wacce ita kuma juyin mulkin soji na watan Yuli ya haddasa dakatar da ita.

Gaba daya wasannin kakar bana za'a yi su ne ba tare da 'yan kallo ba.

Kungiyar Al Masry za ta buga wasanninta a garin Suez, yayin da fitattun kungiyayon birnin Cairo Al Ahly da Zamalek za su buga wasanninsu a barikin soja ne.