Manchester City ta zama ta biyu

Image caption Vincent Kompany ne ya farke kwallo

Tazarar maki daya ne tsakanin Manchester City da Arsenal mai jagorantanr rukunin Premier bayan da ta yi nasara kan Liverpool a fafatawar da suka yi a filin Etihad.

Liverpool ce kan gaba a teburin ranar Kirsimeti kuma bayan nasara Arsenal a West Ham za ta iya ci gaba da rike matsayin da ta zama kungiya ta farko a bana da ta doke City a gida.

Philippe Coutinho ne ya fara tura su gaba kafin kyaftin din City Vincent Kompany ya farke.

City ta samu nasara ne kafin tafiya hutun rabin lokaci lokacin da golan Liverpool Simon Mignolet ya yi sakaci da kwallon da Alvaro Negredo ya buga masa.

Duk da haka dai Liverpool ta yi rawar gani a wasan kodayake Raheem Sterling ya barar da damarmaki da yawa.