Suarez ya cika lambo - Mourinho

Image caption Jose Mourinho wanda ake kira 'The Special One'

Kocin Chelsea Jose Mourinho, ya zargi dan kwallon Liverpool, Luis Suarez da yin lambo a wasan da su ka samu nasara daci biyu da daya.

Suarez ya fadi kasa a cikin da'ira na 18 lokacin da ya hade da Cesar Azpilicueta, abinda ya sa 'yan Liverpool ke ganin kamata yayi a basu bugun fenariti.

Mourinho yace" Babu matsala a kwallon, kawai don Azpilicueta ya kwace kwallonne shi yasa Suarez ya fadi kasa."

Sai dai shi kuma kocin Liverpool, Brendan Rodgers na cewar kamata yayi a kori Samuel Eto'o daga cikin wasan saboda kayar da Jordan Henderson, inda suka samu bugun tazara har suka samu kwallonsu ta farko ta kafar Skrtel.

Dan kwallon Uruguay Luis Suarez, ya ci kwallaye 19 cikin wasanni 14, bayan dakatarwar da aka yi masa sakamakon cizon da ya yi wa dan kwallon Chelsea, Branislav Ivanovic.

Yanzu Chelsea ce ta uku a kan teburin gasar premier a yayinda Liverpool ta koma matakin na biyar.

Karin bayani